KannywoodLabarai

Yanzu-Yanzu Hamisu Breaker Ya Bayyana Gaskiyar Magana Akan Soyayyarsa Da Rakiya Musa | Hadiza Gabon

Bayan abinda yake faruwa bayan Jaruma Hadiza Gabon Tayi hira da Jaruma Rakiya Musa inda a hirar ne Hadizan tayiwa Rakiya tambaya, ko an taba yaudarar ta a soyayya? Anan ne Rakiyan ta zubar da abinda yake ranta akan soyayyar da take yiwa wani bawan Allah, wanda kuwa bata samu nasarar samun soyayyar sa ba, inda tana maganar tana kuka.

Bayan wannan hira mutane sun tausayamata sosai inda suke ganin ba kowa bane wannan masoyi sai Hamisu Breaker, wannan magana ta cewa Hamisu Breaker Rakiya ke nufi a maganganun ta sun tashi hazo inda maganar ta karade safukan sada zumunta, wasu na zargin Breaker da yaudarar Rakiya Musa, wasu kuma na rokon Breaker da yayi hakuri ya aureta.

Daga karshe dai Hamisu Breaker yayi magana akan wannan al’amari inda ya nuna cewa; maganar da Rakiya Musa tayi na an yaudareta bashi bane, har ya kara da cewa; Babu soyayya a Tsakanin su saidai mutunci. Kamardai yanda yake cewa.

 

Assalamu alaikum masoyana tare da fatan kun sha ruwa lfy dazu wasu daga cikin masoyana suka ja hankali akan wannan batun da yake ta yawo cewa Rukayya Yusuf ƴar Asalin Niger wadda Hadiza Aliyu tayi hira da ita wasu mutane na cewa wai dani tayi soyayya kuma har na juya mata baya.

Sam Sam wanna maganar ba haka take Hasali ma ni babu wata alaƙar soyayya tsakanin mu sai dai Mutunci.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button