Labarai
Jami’an Yan Sanda Sun Kama Masu Zanga-Zanga Mabiya Shi’a A Abuja
Jami’an Ƴan Sanda Sun Kama Mabiya Shi’a 19 Da Suka Yi Zanga-Zanga A Abuja Taskar nasaba ta rawaito Jami’an yan sanda sun kama wasu mabiya kungiyar Shi’a (IMN) 19 Sakamakon kamsu da laifin kawo cikas da tayar da zaune tsaye, da kuma jerin gwano ba bisa ka’ida ba a Babban birnin tarayya Abuja. Hakan dai ya biyo bayan hukuncin da babbar kotun tarayya ta yanke kan sakin shugaban kungiyar, Sheikh Ibraheem El-Zakzaky da matarsa, Zeenah ba tare da basu fasfo ɗin su na kasa da kasa ba. Sama da mambobin kungiyar 400 ne suka gudanar da zanga-zanga daga babbar kotun tarayya zuwa dandalin Eagle Square da ke Abuja. Sun kuma toshe hanyoyin, wanda hakan ya batawa jama’a rai, musamman matafiya. kuma sun bukaci a gaggauta sakin fasfo din shugaban nasu. Wata sanarwa ta musamman da kakakin rundunar ‘yan sandan babban birnin tarayya Abuja, Josephine Adeh, Sufetan ‘yan sanda (SP) ya fitar a daren jiya ta ce, an tarwatsa haramtacciyar muzaharar ne, yayin da aka kama mutane 19 da ake zargi. Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a TaskarNasbaa.Com
