Labarai
Jaririn Da Aka Haifa Rike Da Abun Kayyade Iyali A Hannun Shi
Matar Aure ta Haifo Jariri Rike da Abun Tsarin Iyali Bayan ta Daure Mahaifa Kada ta Haihu. Wata mata mai shekaru 20, Violet Quick da mijinta John Francis sun gano da yadda suke shirin tarbar 'dan su na farko duk da tsarin iyalin da suka yi. Sai dai, an ga yadda jinjirin nasu ya zo duniya dauke da maganin kayyade iyalin da mahaifiyarsa ta dauki watanni da rufe mata kofar mahaifarta da shi. Matar ta bayyana yadda ta yi fama da laulayi wanda hakan ya janyo hankalinta don yin gwajin juna biyu inda likitoci suka tabbatar ma ta da hakan. Wannan mata mai shekaru 20 da ta samu juna biyu yayin da ta ke amfani da maganin hana haihuwa. ta haifo wani jinjiri wanda ya shigo duniya dauke da abunda take amfani dashi don rufe mahaifa da shi tsarin iyali kenan a hannunshi.
