Uncategorized

Asiri Yatonu Ankama Tsohon Mataimakin Majalissar Dattawa Da Matarsa Kan Laifin Safarar Sassan Jikin Dan Adam

An Kama Tsohon Mataimakin Majalisar Dattawa Da Matarsa Kan Laifin Safarar Sassan Bil’adama Taskar Nasba ta rawaito Rahotanni daga kasar ingila sun ce wata kotu ta tabbatar da samun tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawa, Ike Ekweremadu, da matarsa, Beatrice, da laifin safarar sassan jiki a babbar kasar Nan ta Birtaniya. Mutanen biyu tare da diyarsu, Sonia, da wani likita, Dokta Obinna Obeta, an same su da laifin taimaka wa wani matashi, tafiya Biritaniya da nufin cirar sassan jikin sa, shari’ar da aka shafe makonni shida ana yi a Old Bailey. Laifukan sun hada baki ne wajan kawo matashin dan kasuwa mai shekara 21 a Legas zuwa Landan domin amfani da kodarsa, kamar yadda alkalai suka gano a ranar Alhamis. Jaridar Guardian UK ta rawaito mai shari’a Jeremy Johnson, zai yankewa wadannan mutane hukunci nan gaba kadan. Idan za ku iya tuna cewa rundunar ‘yan sandan birnin Landan ta kama Ike Ekweremadu da matarsa ​​tare da tsare su a watan Yunin 2022. An zarge su da hada baki wajen safarar wani mutum dake gararanba zuwa Burtaniya domin ya cirar kodarsa domin dasawa ‘yarsu. Domin samun sauran Shirye-Shiryenmu Kutuntubi TASKAR NASABAA.COM

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button