SIYASA
Tofah, Wata Sabuwa An Fita Da Bola Tinubu Asibiti A Sirrance
Wata Sabuwa: An fita Da Zababben Shugaban Ƙasa Bola Tinubu A Asirce Zuwa Taskar Nasba ta rawaito zababben shugaban ƙasar baba bola Tinubu, mai shekaru 70, zai iya sake samun kansa yana bayyana hakikanin yanayin lafiyarsa da ya dade yana jan hankalin jama’a masu kokwanto. An fita da zababben shugaban kasa Bola Tinubu ya tafi zuwa kasar waje a wata ziyarar sirri da ya yi a cikin dare kamar yadda mukarrabansa biyu wadanda suka bayyanawa jaridar Peoples Gazette wanda sune suka bayyana. Abokan huldar Tashi sun ki bayyana kasar da aka kai Mista Tinubu, amma sun dage cewa ba ya cikin Mummunar jinya kuma nan ba da jimawa ba zai dawo kasar domin cigaba da jiran kujerar shugabancin Kasar ta Nigeria. Sahara Reporters ce ta fara bayar da labarin tafiyar Mista Tinubu a ranar Laraba da yamma, inda kafar yada labarai ta yanar gizo ta ruwaito majiyar ta ta ce an kai sabon shugaban Najeriyar zuwa Turai domin jinya. Sahara Reporters ta kuma Kara dacewa Mista Tinubu, wanda aka ayyana a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasar Najeriya a watan da ya gabata, ya kamu da rashin lafiya bayan shafe watanni ana gudanar da harkokin siyasa ba tare da katsewa ba, wanda ya kai ga karshen yakin neman zabe na shekara. Bayo Onanuga, mai magana da yawun Mista Tinubu, ya fada a wani sako da ya aikewa jaridar The Gazette cewa shugaban nasa ya tafi kasar waje domin hutawa Ne kawai kuma nan ba da jimawa ba zai dawo kasar. Mista bola Tinubu, mai shekaru 70, zai iya sake samun kansa yana bayyana halin lafiyarsa wanda ya jawo shakkar jama’a. A cikin ‘yan shekarun nan, Mista Tinubu ya yi tafiye-tafiyen gaggawa da dama a kasashen waje, ciki har da a karshen watan Janairun 2022 da aka garzaya da shi Landan a lokacin da ake gudanar da yakin neman zaben fidda gwani. A watan Satumbar shekarar nan 2022, Mista Tinubu ya sake komawa Landan, inda aka ce ya shafe makonni da dama yana karbar magani daga likitoci da dama. Ya yarda a wani lokaci cewa yana iya rasa karfin jiki amma ya ce karfin tunaninsa zai isa ya tafiyar da al’amuran kasar.
