Labarai

Kotu Ta Bada Belin Ado Doguwa

Kotun majistaren jihar Kano ya ba da belin Ado Doguwa da ake zargi da hannu a kashe-kashe da tashin hankali a jihar kano An ce akwai hannun Ado Doguwa a mutuwar wasu mutane a ranar zaben shugaban kasa da na 'yan majalisun tarayya a Kano An ba dan majalisar sharuddan da zai bi nan da zuwa wani lokaci har bayan zaben gwamnoni da za a yi a kasar. Yanzu muka samun labarin cewa, kotu ya ba da belin Hon. Ado Doguwa, wani babban jigon siyasar APC kuma dan majalisar tarayya daga jihar Kano Sannan Freedom Radio ta ruwaito. A baya an tsare Doguwa ne bisa zarginsa da hannu a mutuwar wasu tarin mutane a lokacin zaben shugaban kasa da na 'yan majalisu a Kano. An tsare Doguwa ne na tsawon kwanaki biyar bayan da 'yan sanda suka gurfanar dashi a gaban kotun majistare da ke Kano. Sai dai, lauyan Doguwa, Nureini Jimoh (SAN), ya nemi belin wanda yake karewa daga alkalin kotun, Muhammad Nasir Yunusa. Ya bayyana cewa, tsare Doguwa ya yi kama da take hakkinsa na dan adam, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito. A cewar Jimoh, tun da an ce ana zargin Doguwa da hannu a kisan kai da kuma mallakar makamai ba bisa ka’ida ba. kotun majistare bai da hurumin yin shari’ar Sharadin belin Doguwa Bayan sauraran batutuwa, mai shari’a Yunusa ya ba da belin Doguwa tare da ba shi sharadin kawo mutum biyu masu tsaya masa. Hakazalika, ya ce daya daga cikin masu tsayawa dan majalisar dole ya kasance basaraken gargajiya daya kuma ya kasance sakataren dindindin a ma’aikatar gwamnatin tarayya ko ta jiha.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button