Labarai

Wani Fusataccen Sojan Nigeria Ya Kashe Kwamandan Shi Da Wasu Sojoji Guda Biyu

Taskar Nasba Tarawaito wani fusataccen soja dan Nijeriya ya dauki bindiga ya kashe Kwamandansa, da wasu sojoji biyu har lahira, daga bisani ya kashe kansa da a sansanin ‘Forward Operating Base’, Rabah da ke jihar Sokoto. Wannan Sojan mai suna Lance Corporal Nwobobo Chinoso yaksan ce yana aiki a karkashin bataliya ta 223 da ke Zuru a jihar ta Kebbi. an kuma tura shi aiki sansanin Forward Operating Base Rabah din ne, in da wannan lamarin ya faru ne a gidan Kwamandan sansanin a ranar Lahadi. Nwobobo ya bude wuta ne nan take ya kashe Kwamandan FOB, Lt. T.I. Sam-Oladapo, da wasu sojoji biyu ciki har da Sajen Manjo (CSM), Iliyasu Inusa da Private Attahiru Mohammed, daga bisani ya juya bindigar zuwa kansa. Wannan Lamarin dai ya faru ne a ranar Lahadi 5 ga watan Maris na 2023 da misalin karfe 5 na yamma, sannan har zuwa yanzu ba a iya gano musabbabin da yasa aka bude wutar ba. amma ana kaddamar da bincike kan lamarin.Kwamandan runduna ta 8 Garrison da Kwamandan bataliya 26 nan takesuka ziyarci wurin da lamarin ya afku. Hakazalika an kwashe gawarwakin zuwa dakin adana gawarwaki na asibitin koyarwa ta jami’ar Usman Danfodio (UDUTH) da ke babbqn birnin na jihar Sokoto. Anyi kokarin jin ta bakin daraktan sashin yaɗa labarai na rundunar sojin na Nijeriya, Birgediya Janar, Onyema Nwachukwu, amma lamarin ci tura, sai dai wasu majiyoyin soja sun tabbatar wa leadership da faruwar yadda lamarin ya afku.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button