Labarai

Qalau Innalillahi Kunji Wata Sabuwa Kuma:-DA DUMI-DUMI: Majalisar Ƙoli ta goyi bayan manufar sake fasalin Naira

DA DUMI-DUMI: Majalisar Ƙoli ta goyi bayan manufar sake fasalin Naira

Taron Majalisar Ƙoli ta Ƙasa, dokkasar wanda shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jagoranta a yau Juma’a, ya bayar da goyon bayansa ga manufar sake fasalin kudin Naira.

Sai dai kuma majalisar ta yi gargadin cewa gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele da ya samar da sabbin takardun kudi na Naira isassu, tare da barin tsoffin su ma a ci gaba da amfani da su don sauƙaƙa wa ƴan Najeriya radadi.

A yayin ganawa da manema labarai na fadar Gwamnatin Tarayya a karshen taron, gwamnonin Taraba, Darius Ishaku, Legas, Babajide Sanwo-Olu, da babban lauyan gwamnatin tarayya kuma Ministan Shari’a, AGF Abubakar Malami, sun ce gaba daya ƴan Majalisar sun amince da manufar ta CBN, amma sun nuna rashin gamsuwa game da aiwatarwar da manufar.

Ishaku ya ce: “An shawarci CBN da ta samar da kudi da yawa. Haka kuma za a iya sake raba tsofaffin kudaden domin rage wa talakawa radadin wahala.”

Taron, wanda ya dauki tsawon sama da sa’o’i hudu an yi shi ne a zauren majalisar da ke fadar shugaban kasa a Abuja.

Taron ya kuma samu halartar tsoffin shugabannin kasa da su ka haɗa da Janar Yakubu Gowon (mai ritaya), Janar Abdulsalami Abubakar (mai ritaya) da Goodluck Jonathan, yayin da tsohon shugaban kasa , Olusegun Obasanjo, ya halasci ganawar ta yanar gizo.

Su ma tsoffin manyan jojin tarayya, Alfa Belgore da Mahmud Muhammad sun halarci taron.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button