Labarai
Trending

Yanzu-Yanzu._Labari Da Dumi-Dumin Sa:- Bayan Hukuncin Da Kotun Koli Ta Yanke Gameda Tsofaffin Kudi Gwamnatin Tarayya Ta……….

Gwamnatin Tarayya Ta Shigar Da Ƙara Domin Ƙalubalantar Hukuncin Kotun Ƙoli Kan Tsofaffin Kuɗi

Gwamnatin tarayya a ranar Laraba ta shigar da ƙara inda take ƙalubalantar ƙarar da jihohin Kaduna, Zamfara da Kogi suka shigar kan dakatar da wa’adin ranar 10 ga watan Fabrairu, na daina amfani da tsofaffin kuɗi. Rahoton jaridar Daily Trust ya tabbatar.

A cikin ƙarar wacce lauya Mahmud Magaji (SAN) ya shigar, gwamnatin tarayya tace bai kamata ace an kawo ƙarar kotun koli ba saboda akan wata ma’aikatar gwamnatin tarayya ce, kuma CBN yana da ikon janye tsofaffin kuɗi da kawo sababbi a ƙarƙashin kunɗin dokar data kafa bankin ta shekarar 2007.

Gwamnatin tarayyar tayi nuni da cewa babbar kotun tarayya itace ke da hurumin sauraron irin waɗannan ƙararrakin a ƙarƙashin sashin doka na 251(1)(a)(p)(q) da (r) na kundin tsarin mulki.

A yayin da gwamnatin tace matakin da gwamnonin suka ɗauka na zuwa kotun ƙoli ya karya doka, ta kuma ƙara da cewa gwamnatocin jihohin ba su da wani hurumi na ɗaukar wani mataki kan hukuncin ainihi da kotun ƙolin ta fara yankewa.

Kafin gwamnatin tarayya ta ƙalubalanci hukunci dai, a jiya ne kotun ƙolin ta umurni CBN da ya bari a cigaba da amfani da tsofaffin takardun kuɗi na N1000, N500 da N200, har zuwa bayan wa’adin ranar 10 ga watan Fabrairu, inda ta sanya ranar 15 ga watan Fabrairu a matsayin ranar da zata saurari ƙarar.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button