Labarai

Wasu Yan Bindiga Sun Kashe Alkali Ana Tsaka Da Zaman Kotu

Wasu Yan Bindiga Sun Kashe Alkalin Kotu Cikin Kotu Yana tsaka da Yanke Hukunci Wasu miyagun yan bindiga sun bindige Alkali har lahira kuma shugaban kotun kostomaren Ejemekwuru, Nnaemeka Ugboma, har lahira a ranar Alhamis din da tagaba ta.

Wannan lamari ya auku ne a karamar hukumar Oguta dake jihar ta Imo.

Leadership ta ruwaito wani mai idon shaida da cewa yan bindigan sun dira harabar kotun kai tsaye a kan babura kuma suka garzaya kai tsaye cikin kotun ana tsaka da zaman shari’a.

Ya kuma kara da cewa nan take suka fito da alkalin waje kuma suka bindigeshi suka kama gabansu batare da jin wani abu zai biyo bayaba.

Mai idon shaidan wandawa ya bukaci a sakaye sunan shi yace: “Yan bindigan sun iso kan babura, suka shiga cikin kotun kuma suka fito da shi wato (Alkalin) duk da ganin cewa ana kan zaman motu.

A lokacin da Suka bindige shi sun hau kan baburansu ne kuma suka wuce yayin nan ne mu kuma muka zuba da gudu.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button