Labarai

Yan Sanda Sun Kama Wani Barawo Mai Abun Ban Mamaki

Wani barawo mai abin ban mamaki ya shiga hannun jami’an hukuma a jihar Delta,dake kudu maso kudu An rasa ta yadda mutumin wanda ya kusa shekaru 50 a duniya ke sace janareton duk da irin nauyinsa.

Hukuma ta bayyana cewa har yanzu tana gudanar da bincike na musamman kan lamarin don sanin yadda yake yin wannan aika aika ta shi.

Jami’an hukumar yan sanda a jihar Delta sun cika hannu India sukayi ram da wani barawon wanda ya shahara wajan satan manyan janareton kamfanoni a cikin dare.

Kakakin hukumar yan sandan jihar, DSP Bright Edafe, ya bayyana cewa har yanzu sun gaza fahimtar yadda yake iya sace na’ura mai matuakar nauyi irin haka.

Har Yanzu Mun Gaza Fahimtar Yadda Yake Sacesu: Cewar Yan Sandan Da Suka Damke kasirgumin Barawon Manyan Janareto a jihad delta.

Wani jawabin kuma da ya fitar a shafinsa na Tuwita ranar Laraba, DSP Bright Edafe ya bayyana cewa an samu ire-iren wadannan jarareto had guda 15 a hannun shi barawon.

Mun gaza fahimtar ta yadda wannan mutumin yake yi mai suna Titus Sunday dan shekara 49 ta yadda ya kware wajen sace manyan janareto daga gidajen mutane cikin dare, ya fitar da su ta yadda ba’a iya taba kamashi.

An kwato sama da janareto goma sha biyar daga hannun kasurgumin barawon DSP Bright Edafe sannan kuma ya kara da cewa har yanzu ana gudanar da bincike na musamman da zarar sun ga kuma zai bada labarin sakamakon bincike daga baya.

 

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button