Labarai

Wani Matshi Ya Jefa Mahaifin Shi Cikin Rijiya Akan Rigimar Fili

Wani dattijo dan shekara sittin 60a duniya yana can asibiti rai a hannun Allah bayan shafe kwanaki uku da yayi a cikin Rijiya wadda take da tsawon kafa 20 dansa ya jefa shi cikin ta.

Tsohon mai suna Samuel Sanui wanda yafito daga kasar Emitiot Chepalungu dake cikin gundar Bomet, dan nasa yajefa shi cikin rijiyar ne bayan sunyi rigima akan wani fili.

Wata sanarwa da wani jami’i yayi mai suna Lenny Ngeno mahaifin yaki yarda dan nashi mai suna Charles Kiplangat Rochit dan kimanin shekaru 22 a duniya hakan ne ya tuzura shi ya shirya yadda zai hallakar da mahaifin na shi.

 

Rochit yayi tunanin mahaifin na shi ya mutu bayan ya jefa shi a cikin rijiya, dattijon ya cigaba da kuruwa ne inda ya samu yayi wata kara da kyar anan ne aka samu masu wucewa sujiyo shi aka fitar da shi saga cikin rijiyar sannan aka garzaya da shi asibiti.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button