Matar Da Mijinta Yayi Mata Duka Saboda Tayi Hira Da Wani Namiji Facebook

Wata mata mai suna Habiba ta bayyana yadda mijinta ya lakada matamugun duka bayan ya kamata da laifin tana hira da wani namiji a Facebook.
Kamar yadda bidiyon hirar ta da At-Tasfiyya TV ta yi da ita, an ga yadda fuskarta ta ci duka inda ta kumbura suntum ta yadda ba za a iya gane asalin halittarta ba ko kadan sakamakon dukan da taci a hannun mijinta.
Mijin matar ya bayyana cewa bayan shigowa dakinta ne ya tambayeta da wanda take hira a waya, sai ta bayyana masa cewa da abokinta na Facebook take hira.
A cewarta sanar da shi ke da wuya ya hau dukanta kamar Allah ya aiko shi yayimata wannan aika aika, inda mijin matar ya ce dama ya yi zargin da namiji take hira.
Ya ce ba wata alaka bace babba tsakaninta da wanda take hirar da shi, kawai a Facebook ne ya tura mata gayyatar zama kawarsa ita kuma nan take ta amsa daga nan hira ta yi tsawo tsakaninsu.
Ta bayyana cewa abinda ya sa take neman wanda za ta yi hira da shi saboda tana yawan samun matsala da mijinta ne, kuma sam ba sa hira a cewarta.
Kasancewar dare ne yayi sosai, sai ta nemi wanda zai debe mata kewa, hakan yasa ta biye wa matashin suka dinga kwasar hirar su.
Ta ce shekarunsu 10 da aure da mijinta, kuma Ubangiji ya azurta ta da yara guda 4. Ta kuma shaida yadda dama yake dukan maza tun kafin ya aureta duk lokacin da ya ga suna magana da ita.
Ta kuma kara bayyana cewa wannan shine karo na biyu da ya taba dukan ta tun bayan auren su, na farko saboda ta fita bata dawo gida da wuri bane, sai wannan karon na biyu.