Labarai

Peter Obi Zamu Samar Maku Cigaba Da Danyan Man Da Aka Hako A Jihar Bauchi

Dan takarar sugaban kasa Peter Obi Ya Bayyana Abin Da Zai Yi Da Man Fetur Din Da Aka Gano A jihad Bauchi Idan Ya Zama Shugaban Kasa maici a Nigeria, Peter Obi ya kuma dauki alkawarin yin aiki tukuru da kudin danyen man da aka hako a jihar Bauchin don ciyar da Bauchi da Arewa gaba.

Dan takarar na LP, ya bayyana hakane a taron gangamin yakin neman zaben da ya gudanar a Bauchi ranar Alhamis Mr Obi ya kuma bukaci shugabannin kasar nan da su yi koyi da Tafawa Balewa wajen gudanar da mulkinsu don bunkasa Najeriya.

Dan takarar shugabancin kasa wanda yake a jam’iyyar ta LP, Mr. Peter Obi, ranar Alhamis, ya tabbatarwa da alummar Jihar Bauchi cewa za ayi amfani da danyen man fetur din aka samu a jihar don ciyar da jihar da kuma yankin Arewa gaba.

Ya yi alkawarin ne a yakin neman zaben zaben jam’iyyar da ya gudana a filin wasa na Tafawa Balewa a Bauchi, babban birni Jihar Bauchi, da yake a yankin Arewa maso gabashin Najeriya.

Za mu tabbatar an yi amfani da man don cigaban Bauchi, Peter Obi Obi ya ce Mun san abin da yake faruwa a Bauchi a halin yanzu. Muna son yin amfani da wannan dama ta danyen man da aka hako don cigaban Bauchi, da kuma baku ayyukan yi.

Ya kuma kara da cewa zamu tabbatar anyi amfani dashi don cigaban Bauchi, da cigaban Arewa baki days injishi.

 

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button