Labarai

Kwan Kwaso Yace Yan Nigeria Baza Suyi Asarar Tsofaffin Kudinsu

Zan share wa talaka hawaye kan batun sauya takardun kuɗi in ji Dr, Rabi’u Musa Kwankwaso

Sanata Kwankwaso ya bayyana hakan ne ganin yadda talakawa halin da suka shiga a kasar musamman yan kwanaki biyu da suka gaba ta wanda matsalar ce har kawo yanzu itace take damun mutanan Nigeria.

Idan na ci mulki zan bada dama ta mussamn ga kowa ya kai tsoffin kudi banki ba tare da asara ba, in ji Kwankwaso

Sa’o’i 5 kenan da suka wuce
Ɗan takarar shugaban kasa a jam’iyyar NNPP, Injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso ya ce baya goyon-bayan tsarin da aka bi wajen sauya takardun kuɗi a kasar ta Najeriya.

Kwankwaso da ke shaida hakan a lokacin wata tattaunawa da BBC, ya ce yanzu abu guda shi ne mahukunta a kasar suyi kokarin kokarta su kara wa’adin da babban bankin kasar ya bayar na daina amfani da tsoffin takardun kuɗi a kasar.

Injiniya Kwankwanso ya ce al’umma na shan wahala sakamakon canjin kuɗin, don haka ya kamata gwamnati ta sassauta talakawan ta injishi.

Kalaman ɗan takaran na zuwa ne kwanaki kadan wa’adin da babban bankina na Najeriya wato CBN wanda ya bayar na daina karban tsoffin takardun kuɗi ya cika.

Sai dai dan takarar ya ce idan gwamnatin APC mai Mulki ta ƙi kara wannan wa’adin talakawa kada kowa ya ta da hankalinsa

Injiniya Kwankwaso ya ce masu tsofaffin kuɗi su ajiye kudinsu, idan ya samu nasarar zama shugaban kasar nan ta Nigeria zai bai wa kowa damar canja kuɗinsa ba tare da kwabonsa ya yi ciwon kai ba ko guda daya.

Ya kamata a kara wa’adin daina karbar tsoffin kudi a Najeriya inji kwan kwaso
Ina jin bakincikin ganin yadda ake wahalar da talaka.

Kwankwaso ya kara da cewa su dai nasu bai wuce bai wa gwamnati hakuri ba da kuma bada shawara na ta dubi talakan kasarta Najeriya ta jikansu kada mutane su yi asarar kudadan su.

Musamman akai duba daTalaka na arewa suna cikin masifa da matsi na rayuwa da kullum ake ganin sabon salo.

Sannan kuma Kwanwkaso ya ce idan gwamnati tayi biris bata duba ba to zai yi fatan Allah yaba shi nasarar lashe zaɓen bana domin ya maidowa kowane mutum halaliyar sa ba tare da ko kobonsa ya tabuba.

 

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button