SIYASA
Trending

Ran Maza Ya Baci:-Majalisa za ta umarci ‘yan sanda su kamo Gwamnan CBN Emefiele

Majalisa za ta umarci ‘yan sanda su kamo Gwamnan CBN Emefiele

Kakakin majalisar wakilan Najeriya Femi Gbajabiamila ya ce ba zai yi kasa a gwuiwa ba wajen neman Sufeto-Janar na ‘yan sandan Najeriya Usman Baba ya fitar da sammacin kama Godwin Emefiele, wanda shi ne gwamnan babban bankin kasar.

Wannan gargadin ya biyo bayan kin bayyana gaban majalisar a dalilin gayyatar da ta mika wa gwamnan. Mista Gbajabiamila ya sanar da haka ne a ranar Alhamis bayan da Alhassan Doguwa, shugaban masu rinjaye na majalisar ya gabatar da rahoton kwamitin majalisar bincike kan ayyukan banki na kasar.

Alhassan Doguwa ya sanar da majalisar cewa Mista Emefiele bai bayyana a gaban kwamitin ba kamar yadda aka bukace shi yayi a ranar Laraba.

A nasa bayanin da ya gabatar, Mista Gbajabiamila ya ce a shirye yake ya yi amfani da sashe na 89(1)(d) na kundin tsarin mulkin Najeriya wanda ya ba majalisa ikon umartar jami’an tsaro su kamo wanda ya ki bayyana a gaban majalisar.

Sai dai Mista Emefiele ya bayyana cewa matsalar da aka kira shi akai ta karancin sababbin takardun kudi ce, kuma alhakin haka ya rataya ne a wuyan bankunan kasuwanci na kasar.

Ya kuma kafe cewa ba zai tsawaita kwanakin da bankin ya tanadar wa ‘yan Najeriya su sauya tsofaffin takardun kudinsu da sababbin ba.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button