Labarai

Yan Sanda Sun Kama Maiba Yan Bindiga Bayanan Sirri

A jihar katsina Ƴan Sanda Sun Yi Nasarar Cafke Mai kaiWa Ƴan Bindiga Bayanan Sirri A Katsina

Rundunar yan sandan jihar Katsina karkashiin jagoranci Kwamishinan Ƴan Sanda na jihar, Alhaji Shehu Umar Nadada ta yi nasarar cafke mai kaiwa yan bindiga bayanan sirri, mai suna Yunusa Sani, dan shekara 21 da haihuwa dake Unguwar Rigasa a jihar Kaduna.

Bayanin hakan dai na kunshe a cikin wata takardar manema labarai da jami’in hulɗa da jama’a na rundunar SP Gambo Isa ya fitar, aka raba wa manema labarai a Katsina da yammacin yau Talata.

Takardar ta kuma kara da cewa jami’an rundunar tare da haɗin gwiwa da yan sa kai da ke garin Unguwar Nakaba a karamar hukumar Sabuwa ta jihar Katsina suka gudanar da aikin.

A cikin binciken da rundunar ta yi wanda ake zargin ya amsa laifinsa kuma ya bada bayanai ga yan bindiga, su sace Malam Shu’aibu da Malam Haladu da Baba Sa’idu da kuma Suleman Doguwa, duk yan garin Unguwar Nakaba a karamar hukumar Sabuwa ta jihar Katsina.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button