Labarai
Trending

Da Dumi-Dumin Sa:-Majalisar dokokin Najeriya Zata Sharewa Talakawa Kukan Su kan Karancin Sabbin Kudi.

Majalisar dokokin Najeriya na neman shugabannin bankuna don tattaunawa dasu kan karancin kudi da ake fama dashi a bankuna

du

FCT, Abuja – Yayin da ‘yan Najeriya ke ci gaba da samun karancin kudi a bankunan kasar nan, majalisar dokokin kasa ta yi yunkurin samar da mafita.

Majalisar ta gayyaci shugabannin bankuna a kasar nan don ba da bahasin dalilin da yasa ba a samun sabbin takardun Naira da aka buga a banki, BBC Hausa ta ruwaito.

 

A cewar rahoton da muka samo, an ce shugabannin bankunan za su bayyana ne a gaban majalisar a ranar Laraba 25 ga watan Janairun da muke ciki.

 

Majalisa Za Ta Zauna Shugabannin Bankunan Kasar Nan Don Magance Karancin Sabbin Naira | Hoto: David Darius Asali: Getty Images Ganawar za ta kasance ne tsakanin kwamitin majalisa kan bakuna karkashin jagorancin shugaban masu rinjaye, Alhassan Ado-Doguwa. DUBA:

 

Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

 

Ana neman mafita ga matsalar kudi a Najeriya A bangare guda, majalisar ta yanke shawarin gayyatarsu ne domin tattaunawa don samu mafita ga karancin kudin da ake samu a kasar. Hakazalika, rahoto ya bayyana cewa, daga baya za a gayyato shugabannin CBN domin su ma su ba da bahasi game da halin da ake ciki.

 

Game da wa’adin mayar da tsoffin kudade kasar, majalisar ta kuma bukaci CBN ya kara wa’adin zuwa karshen watan Yulin bana.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button