Labarai

Wasu Yan Bindiga Sun Kaiwa Dan Takarar Gwamna Hari A Jihar Robas

Wasu miyagun yan ta’adda ɗauke da bindigu sun farmaki dan takarar gwamna na Accord Party a jihar Ribas ranar Asabar 21 ga watan Janairu.

Chief Dumo Lulu-Briggs, shi ne ya tabbatar da lamarin da kansa ya ce yana hanyar zuwa Sakatariyar Accord da ya samu labarin an kai hari Ya bayyana cewa yayin da ya yi kokarin kiran wayan kwamishinan ‘yan sanda na Ribas ba ta shiga ba.

Wasu tsageru sun farmaki ɗan takarar gwamna karkashin inuwar jam’iyar Accord Party a jihar ta Ribas Chief Dumo Lulu-Briggs, a yankin ƙaramar hukumar Etche ranar Asabar.

Jaridar Tribune Online ta tabbatar cewa yayin harin da yan bindigan suka kai an yi kaca-kaca da motar dan takarar wacce harsashi ba ya iya fasawa.

Miyagu Sun Farmaki Dan Takarar Gwamna a Jihar Ribas, yayin da sukaTafka gagarimar Barna Mista Lulu Briggs da kansa ne ya tabbatar da faruwar lamarin.

inda ya ce bayan ya samu labarin an kai hari Sakatariyar Accord Party dake garin Etche ya ɗauki haramar zuwa gani da idonsa.

Dan siyasan ya bayyana cewa a hanyarsa ta zuwa ne yan bindigan suka bude masa wuta tare da magoya bayan da suke masa rakiya.

 

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button