Labarai

Wani Dalibin Jami’ar Fasaha Ya Kashe Kan Shi Ta hanyar Kataya

Wani dalibin jami’ar fasaha tarayya dake Akure jihar Ondo dake Nigeria,dalibin dan aji uku matashin ya rataye kansa acikin daki shi.

Kamar yadda rahoto yazo cewa abokanan matashin sune sukaje dakin abokin nasu inda suka tararda dakin abokin nasu akulle sun kumayi yinkurin bude dakin na shi ta hanyar buga mashi kofa amma hakan batasamu ba sun kuma balla kofar dakin matashin nan take.

Inda bude kofar keda wuya sai sukaga abokin nasu ya rataye kanshi wanda inda dubawar su keda wuya ashe rai yayi halin shi.

Dalibin dai wanda ya kasan ce dan makarantar jami’ar dake koyar limin fasaha ya maida hankali ne wajan koyan fasahar zane-zanen kayayyaki.

Mai magana da yawun yan sandan jihar Misis funmilayo Odunlami, itace wadda ta tabbatar da faruwar wannan al’amari.

Tace suna gudanar da bincike na musamman kuma ayanzu haka ankai gawar dakin ajiye gawar waki.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button