Labarai

Masarautar Katsina Tasake Korar Wani Hakimi Bisa Zargin Shi Da Taimakawa Yan Ta’adda

Masarautar Katsina ta kori Makaman Katsina, wanda ya kasance hakimin Bakori, Idris Sule Idris, kan zarginsa da hannu a ta’addanci.

Korar dai da aka yi wa Idris Sule Idris na zuwa ne bayan wani kwamitin da gwamnatin jihar ta kafa don yin bincike na musamman ta same shi da laifi bayan mutane sun yi korafi
A baya, gwamnatin na Katsina ta taba korar Sarkin Pawan Katsina, hakimin Kankara, Yusuf Lawal, shima kan alaka da ta’addanci

Hakanan masarautar Katsina ta tabbatar da korar babban hakimi, Makaman Katsina, hakimin Bakori, Idris Sule Idris, kan zargin yana taimakawa yan ta’adda domin angano da hannu shi a ta’addanci da akeyi a yankinsa.

Korar tasa na cikin wata wasika ne mai kwanan wata na 19 ga watan Janairun 2023, dauke da sa hannun Kauran Katsina hakimin Rimi, Aminu Nuhu Abdulkadir, wanda shine ya kasance mai nada sarki ne kuma babban mamba na masarautar.

Ba wannan bane karo na farko da aka korar masu sarautan gargajiya da ke ta alaka da yan ta’adda ba.

A shekarar 2021, masarautar Katsina ta kori Sarkin Pawan Katsina, hakimin Kankara, Yusuf Lawal shima kan zarginsa da tallafawa yan ta’addan yankin.

 

 

 

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button