Labarai

Wani Malmin Coci Da Matar Shi Sun Mutu Awajan Ceto Dansu

Idan ajali yazo dole a bar duniya, wani Fasto da matarsa sun rasa ransu yayin da suka kaiwa dansu Agajin gaggawa a cikin wata Teku Bayanai sun nuna cewa ma’auratan yan kasar Brazil sun gamu da Ajalinsu ne daga shiga ruwan don taimaka wa yaron

Babban dan Mamatan yace kafin faruwar lamarin da kwana 2 ya haɗu da iyayensa a she karo na karshe kenan Malamin Cocin dai na kasar Brazil, Felisberto Sampaio, tare da mai dakinsa, Inalda, sun rasa rayuwarsu yayin da suka yi kokarin ceto ɗansu mai shekara 13, inda daga nutsewa a ruwa sun rasa rayiwar su nan take.

Iyalan gidan Faston sun fita zuwa bakin Tekun Camacari da ke João Pessoa, jihar Paraiba domin shakatawa sai dai fitar ta zama itace ta karshe yayin da suka hangi ɗansu a ruwa yana fafutukar neman tsira. Allah sarki malamin da Matarsa Sun Mutu Yayin Kokarin Ceto Dansu Daga Nutsewa a Ruwa.

Taskar Nasaba ta rawaito cewa a kokarin su nakubutar da ɗansu, ma’auratan ba tare da tunanin wani abuba suka yi tsalle suka fada Tekun domin ceto yaron su daga hallaka A yayin da Wasu masu kamun Kifi ne suka yi nasarar tsamo yaron daga ruwa tare dan gidan Faston.

Sannan daga baya masu kamun kifin suka koma nemo Malamin da matarsa, suka dauko su a cikin dan Kwale-kwalensu zuwa bakin gabar Tekun. Bayan fito da su, bayanai sun tabbabatar cewa sai da ma’aikatan jinya suka sanya Fasto Filiberto, dan kimanin shekara 43 da matarsa mai shekaru 42 a cikin CVR domin ceton rayuwarsa. Sai dai duk da haka daga baya Likitocin suka tabbatar da cewa ma’auratan sun riga mu gidan gaskiya, kamar yadda jaridar Taskar Nasaba ta rawaito.

Rahotanni sun bayyana cewa lamarin ya faru ranar Talata 10 ga watan Janairu, 2023. Babban dan mamatan, Isaac ya ce ranar 8 ga watan Janairu ya ga iyayensa bai san haɗuwarsu ta karshe kenan ba.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button