Yadda Wani Matashi Yake Sana’ar Wanke-Wanke

Wani matashi Mai Sana’ar Wanke-Wanke a Turai da Ke Samun kudi Sama da N1m Ya Gigita Jama’a Wani dan kasar Ghana da ke zaune a Jamus ya yi karin haske game da aikin da yake na wanke-wanke a kasar ta Turai A wata hira da aka yi dashi, Kofi Asiedu ya bayyana irin tagomashin da yake samu daga fara sana’ar tashi ta wanke-wanke.
Labarin wannan bawan Allah dai bai tsaya iya nan ba, mutane da yawa sun yaba masa bisa jajircewa da kuma rashin raina sana’a Wannan bawan Allah dai ya kasance dan kasar Ghana a yanzu kuma mazaunin Jamus yana gudanar da sana’ar tashi ne a kasar turai ya kuma karin haske game da sana’ar da yakeyi ta wanke-wanke a kasar ta jamus, ya bayyana yadda yasamu alkhairi a cikin sana’ar wanke-wanke.
Wani babban mutumin ya bayyana cewa yakan samu £12 a duk sa’a daya, kuma yakan yi aikin sa’o’I takwas(8) ne kacal a rana na tsawon kwanaki 5 a mako. Sai dai, ya kara da cewa mutane kada su yaudaru da yawan kudin, domin a cewarsa, wanke-wanke sana’a ce da ke bukatar natsuwa da kwarewa har ma da juriya.