Labarai

Yan Sanda Sun Kama Mutanan Da Ake Zargi Da Safarar Mutane 41

Rundunar ‘yan sanda a jihar Kwara sun kama wasu mutum hudu da ake zarginsu da sun sato yara daga nan Arewaci za’akai su izuwa Kudu, An kama su tare da yara arba’in da daya (41) suna shirin kaiwa wani faston da ba a bayyana sunansa ba.

A yanzu haka ana ci gaba da bincike, kuma za a tabbatar da an gurfanar da wadannan muta me da ake zargi da aikata wannan munanan laifukan a kotu, Ilorin, jihar Kwara Rundunar ‘yan sandan jihar ta Kwara ta ce ta kama wasu mutum uku ne da ake zargi da aikata safarar mutane daga jihar Neja zuwa birnin Ilorin.

Bayanan sun fitone a wata sanarwa kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Osakanmi Ajayi ya fitar a Ilorin a ranar Asabar, inda ya bayyana yadda lamarin ya faru.

Yan Sandan dai na Jihar Kwara Sun samu nasarar Kama wanda Ake Zargi da Laifin Safarar Mutanen wanda kimanin su yakai yawan arba’in da daya A cewar kakakin rundunar yan sanda an kame wadanda ake zargin ne a kusa da babban titin Okolowo a ranar Asabar tare da yara 41 da suke jiran a kai su wani wuri da ba a sani ba.

Wani bangaren sanarwar ya ce Yaran da aka saton suna da mabanbanbtan shekaru daga biyar zuwa 15.” Yadda suka tsara aikata laifin Ya kuma bayyana cewa, yayin da aka yi bincike, an gano wadanda ake zargin sun tsara haduwa ne a birnin Ilorin bayan tasowa daga jihar Neja domin mika su ga wani fasto

Kwamishinan yan sandan kuma yakara da cewa nan kusa za mu tuntubi iyayensu da sauran hukumomin da suka dace. Kwamishinan ‘yan sandan jihar Kwara, Paul Odama na ba da shawari ga iyaye da masu rike da yara da su guji sakin ‘ya’yansu ga wadanda basu sani ba.

Watakila za a yi amfani da yaran ne a matsayin ‘yan aiki da kuma wasu ayyukan wahala wadanda hakan ya saba dokar hakkin yara za a gurfanar da wadanda ake zargin bayan kammala bincike yadda ya dace.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button