Labarai

Gobara Ta Tashi A Wani Babban Gidan Mai Na AA Rano

Gobara Ta Tashi a Gidan Man AA Rano a Abuja, Babban Wani gidan man Fetur AA Rano da ke kan Titin Lokoja-Abuja tare da kuma wata babbar motar dakon mai a gidan sun kama da wuta, Rundunar yan sandan Abuja ta wajan mai magana da yawunta ta ce jami’an kwana-kwana da yan sanda sun dira sun zagaye wurin nan take.

Josephine Adeh, ta shaidawa Taskar Nasaba cewa jami’an ba da agajin gaggawa sunyi kokarin kashe wutar da kuma dakile rasa kadarorin al’umma masu dunbin yawa, Gidan siyar da man Fetur din dai ya kasance mallakin fitaccen dan kasuwan nan, AA Rano da ke kan Babban Titin Lokoja A Abuja

Gigan man ya kama da wutane a ranar Lahadi, 15 ga watan Janairu, 2023. A wata sanarwa ta misamman da rundunar yan sandan birnin tarayya Abuja tayi ta shai dawa Taskar Naaaba cewa jami’an yan sanda da jami’an hukumar kwana-kwana sun isa wurin a kan lokaci.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button