Labarai
Wata Mummunar Gobara Ta Hallaka Hedikwatan Yan Sanda A Kano

Taskar Nasaba ta rawaito an samu afkuwar wata mummunar gobara da ta tashi a hedikwatar yan sanda dake unguwar Bompai a nan jihar kano.
Gobarar dai ta tashi ne daga ofishin provost sannan daga bisani gobarar tamamaye sauran lungu da sako dake hedikwar na yan sandan, wanda tahada da ofishin kwamishin nan yan sandan A dimin da sauransu.
Gobarar takone duka saman benan dama inda shelkwata ofishin kwamishi nan ne kawai ya samu tsira daga wannan iftila’i.