Magoya Bayan Jam’iyyar PDP Sun Rasa Ransu A Hatsrin Mota

Magoya Bayan jam’iyyar PDP Da Dama Sun rasa ransu Sakamakon Hatsarin Mota Wasu magoya bayan jam’iyyar PDP sun rasu sakamakon hatsarin mota a ranar Asabar Rahotanni sun bayyana cewa lamarin ya faru a kusa da gadar Panyam Tawagar yakin neman zaben dan takarar gwamnan Plateau ta tabbatar da afkuwar lamarin, ta yi ta’aziyya, Magoya bayan jam’iyyar Peoples Democratic Party, PDP, a jihar Plateau da dama sun rasu sakamakon wani hatsarin mota da ya faru a karamar hukumar Mangu.
Taskar Nasaba ta shaida cewa An gano cewa magoya bayan suna hanyarsu na dawowa Jos ne daga wata ralli da aka yi a karamar hukumar Pankshin a lokacin da babban mota ta yi karo da su a Panyam. Magoya Bayan PDP Da Dama Sun Mutu Sakamakon Hatsarin Mota.
Wani mazaunin garin Panyam, Joy Stephen, wanda ganau ne ya shaidawa Taskar Nasaba cewa a ranar Asabar din mutane da dama sun mutu nan take yayin da wasu kuma suka jikkata, Stephen ya ce: “Misalin karfe 4.30 na yamma ne hatsarin ya faru. “Babban motan na dauke da yara maza da mata, suna hanyar zuwa Jos. Wadanda ke ciki magoya bayan PDP ne da ke dawowa daga ralli a Pankshin.
ban san abin da ya faru ba amma motar ta fadi ta kashe wasu yayin da wasu suka jikkata, An kwashe wadanda abin ya faru da su zuwa asibiti a lokacin da muka isa wurin. “Hadarin abin bakin ciki ne domin an yi taron siyasan lafiya kalau.
Jam’iyyar PDP ta tabbatar da afkuwar lamarin Wani sanarwa daga tawagar watsa labarai na dan takarar gwamna na PDP, mai dauke da sa hannun Manga Wamyil, da aka fitar a yammacin ranar Asabar ta tabbatar da afkuwar hatsarin.