Labarai

Wata Mata Ta Hallaka Yaranta Biyu

An kama wata mata da mijinta bisa zargin yiwa ‘ya’yansu biyu kanana ‘yan shekara 5 da kuma ‘yan shekara 2 dukan tsiya.

Rundunar ‘yan sanda a jihar Legas ta damke wannan mata da wata abokiyar zamanta da ake zargin su da yiwa ‘ya’yanta biyu masu masu kananan shekaru year kimanin shekara 5 da dakuma dan shekara 2 dukan tsiya.

Mater dai mai suna Busola Oyediran da abokin aikinta, Akebiara Emmanuel, yan sanda tuni sun kama su a ranar Juma’a nan da tagabata 13 ga watan Janairu hakan yabiyo bayan ne bayan da wani rahotannin da makwabtan su suka bawa yan sanda.

Wannan makwabtan da abin ya shafa sun bayyanawa ‘yan sanda irin muzgunawa da cin zarafin da ake na kananan yara wanda mahaifiyarsu ce take aikata masu tare da ita da abokin zamanta, jinhakan keda wuya ‘yan sanda suka zagaye gidan wannan magidanta, Egbeda/Idimu yanzu haka dai suna hannun yan sanda sannan kuma daga bisani ‘yan sandan sun samu ziyarci asibitin da aka kai yaran domin a sama masu lafiya.

Yan sandan sun tambayi mahaifiyar dan suji daga bakinta nan take ta bayyana masu cewa yaran sun fadone daga saman babur shi ne yasa suka samu raunuka.

SP Benjamin ya shaidawa manema labarai Iyayan wannan suna tsare a hannun su, a halin yanzu kuma za a gurfanar da su a gaban kotu.

TASKAR NASABA

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button