Labarai

An kama kwamishinan Dan Sanda Nabogi Ya Damfari Wani Mutum Miliyan 250

A jihar legas ne aka samu wani kwamishinan dan sanda na bogi mai suna Oluwele Akande dan kimanin shekara hamsin da biyar da haihuwa 55 wannan mutumi dai a nazargin shi ne dayin basaja a matsayin kwamishinan yan sanda nabogi.

Asirin shi dai yatonu bayan da akasame shi ya damfari wani dattijo dan kimanin shekara tamanin da takwas 80 zun zurutun kudi har naira miliyan 250,
Kwamishinan yankin CP Yetude Longe shine ya babbatarwa kamfanin dillancin labarai na kasa hakan cewa sunkama wanda a kezargi

Longe tace tasamu kira daga CP frank MBA tsohon mai magana da yawun rundunar akan lamarin,
Inda ta bayyana cewa matar wanda ake zargi itace takira CP frank MBA domin tatsegwanta masa abun da wani CP Longe keyi naneman mijin nata ya bashi milyoyin naira, domin takashe wata kara da aka kaimata akan mijin nata.

Nan take CP frank ya amsawa matar wanda abun yashafa ya kuma ce yasan CP yetunde longe bazata aikata wannan mummunar bukatarba, amma zaije ya tabbatar sannan daga bisani yadawo wajan matar.

Tace CP frank ya kirani don inbada bayanin yadda abun yafaru kumana tabbatar masa cewa babu wani korafi a gabana kuma basan wanda abun ya shafaba.

Tuni dai aka mika lamarin wajan CID panti sun kuma kama wanda ake zargin, kwamishinan tace nan bada jimawaba zasu gurfanar da shi a gaban kotu.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button