Labarai
Trending

Hukumar JAMB Ta Saka Ranar Fara Siyar da Fom din UTME.

Hukumar JAMB Ta Saka Ranar Fara Siyar da Fom din UTME

Hukumar Shirya Jarrabawar Shiga Jami’a (JAMB) ta fara sayar da takardun neman shiga manyan makarantun gaba da sakandire na shekarar 2023 a Najeriya da kuma cibiyoyin kasashen waje. Kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Ana gayyatar aikace-aikacen daga daliban da suka cancanta don shiga jarabawar zuwa Manyan Makarantu a Najeriya don neman Ilimin a shekarar 2023.

Lokacin da aka warewa masu yin rajista don UTME kawai shi ne:

Lokacin yin rajista na masu neman UTME ciki har da waɗanda suka fito daga ƙasashen waje, za a fara shi ne daga ranar Asabar 14, gawatan Janairun shekarar 2023 zuwa Talata 14 ga Fabrairu, 2023.

Yayin da za a rufe Siyar da PIN don UTME a ranar Talata 14 ga Fabrairu, 2023, za kuma a rufe rajista ne a ranar Juma’a, 17, 2023.

Lokacin rajista don Jami’o’i kai tsaye wato DE

Dole ne daliban su sami ingantaccen adireshin imel na su na kansu, mai aiki kafin fara aikin ragistan. Da dai sauran su.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button