Labarai

Ankama Wasu Mutane Uku Suna Kokarin Sace Gawar Fir’auna

Tofa anan kuma wani rahoto mukasamu daga kasar masar inda rahoton yake bayyana mana cewa ofishin mai shigar da kara na kasar masar shine ya bayyanawa manema labarai ceawa wadansu mutane guda uku 3 ne sukayi kokarin sace (gunki)ma’ana mutum mutumin fir’auna,wanda kekudancin birnin Aswan dake kudancin kasar wanda keda tazarar da yakai kilomita 675 da birnin Cairo nafadar gwamnatin.

Masu satar dai sunyi amfani da katon injin daukar kaya wajan satar tuni dai ofishin ya ware shafin bincike nakwana uku domin tabbatar da manufar su ta kokarinsu nasace gunkin fir’auna mai matukar tarihi.

rudunar yan sandan kasar sun damke mutum ukun da akezarginsu suna kokarin sace gunkin na fir’auna, an samu mutanan ne da tarin kayan haka masu nauyi da kuma babban injin daukar kaya yansandan sunce dazarar bincike yakammala zasu gurfanar dasu a gaban kotu.

bayan haka kuma ofishin mai shigar da kara na kasar masar din ya bukaci da anemo duk wanda kedasa hannu acikin wannan aiki nadauke gunkin mai dinbun tarihi.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button