An Cirewa Wata Kyanwa Kullin Gashi A cikin Ta Har Guda 38

Wani mutum mazaunin yankin amerika ya bayyanawa gungiyar kula da hakkin dabbobi Charleston animal society cewa wannan kyanwa mai suna juliet yaganta ne a wani gida inda asalin tsofaffin masu gidan suka tashi sukakoma wata jiha.
Wannan mutumin ya lura cewa wannan kyanwa batacin abinci nawasu yan kwanaki da dama shine sai ya daukota yakawota asibiti inda likicocin dabbobin suka tabbatar masa cewa sun gano a kwai waniabu da ya cushe mata a cikin ta.
Leigh Jamison shine wanda ya kasance darakta a asibitin dabbobi ya kuma bayyanawa manema labarai cewa shi tunda yake baitaba ganin irin wannan Abu ba a rayiwar shi, likitocin da sukayimata aikin tiyatar sun rikice akan ganin abunda ya cushe mata ciki domin kuwa kullullukan gashi ne har guda talatin da takwas 38
Yanzu daraktan asibitin dai wato jamison yace kyanwar mai suna Juliet tana samun sauki kuma yakara da cewa gashin da suka cushemata cikin hakan ya janyomata matsalar da takai ga tabamata kodarta
sannan kuma yakara da cewa ma’aikatan mu suna bata kulawa tamusamman wajan ganin lafiyarta tadawo.