Labarai
Trending

Wani Ango ya rasu ana daf da ɗaura masa aure a jihar Katsina:- Innalillahi Wainna Ilaihirrajuun😭

Kamar yadda shafin jaridar Zuma Times Hausa ya ruwaito.

Ango Ya Nesanta Da Duniya Ana Gab Da Ɗaurin Aurensa A Katsina

Daga Zaharaddeen Gandu

Wani matashin Ango ya rasu ana gab da ɗaura masa Aure da Amaryarsa a jihar Katsina.

Abokin karatunsa Kamilu Abubakar shi ne ya bayyana mana haka a wayar salula, inda ya bayyana cewa, motar su angon ta taso daga jihar Nasarawa zuwa jihar Katsina a lokacin ne haɗarin mota ya rutsa da su a daide marabar ƙaramar hukumar Ɗanja dake jihar Katsin, kamar yadda wakilin jaridar Katsina Post ya rawaito.

Wannan lamarin ya faru ne saura kwana 6 a ɗaura Aurensa da Amaryarsa.

Wata majiya mai tushe daga Abokan karatunsa, Comrade Umar Musa Yar’addu’a da Mujahid Rabi’u sun bayyana cewa, sun yi waya da shi a ranar kuma sunyi chat da shi a kafar sadarwa ta Facebook, sun ce a lokacin da ya taho yayi rubutun addu’a a kafar Facebook kafin ya baro jihar ta Nasarawa inda yake cewa yana a hanya Allah ya kawo su gida lafiya.

Kafin rasuwar matashin, ya kammala karatunsa a Kwalejin Ilimi Ta Tarayya dake Katsina (FCE Katsina) a sashen HAUSA/ISLAMIC a 40SERIES.

Angon ɗan asalin garin Kuka-sheƙa ne dake yankin ƙaramar hukumar Malumfashi a jihar Katsina, ya rasu yana da shekaru 24 a duniya muna fatan Allah ya gafarta masa ameen.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button