Uncategorized

An kama Wadanda Suke Shigarwa Da Yan Ta’adda Makamai Cikin Daji

Assalamu alaikum masu saurare rahotanni daga taskar nasaba a ranar asabar din da tagabata ne jami’an tsaro da misalin 12:15 pm yan sanda suka kai same gawasu barayin daji sun kuma samu nasarar cafke motarsu wadda take dauke da makamai manya manyan bindigu dakuma harsashi, wadannan mutane sun kware sosai wajan shigar da makamai zuwa ga yan ta’adda.

Barayin sun kwaso makaman daga jihar taraba zuwa zamfara ,sun iso hanyar gumi zuwa anka dake jihar ta zamfara yan sanda suka masu kwanton bauna suka kamasu biyu daga cikin barayin sun isa lahira nan take.

Yan sandan sun kama motar barayin ne wadda take da kira kamar haka corolla mai launin baki sun kama yimata rijista NIGERIA:SRP702XA harsa shin bindiga kuma kimanin dari hudu 400 an samu makamin roket guda uku 3 da bama bamai guda biyu 2 da harsashin bindiga mai jigida sai kuma kayan tsafi.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button