Wani Matashi Dan Shekarar Ashirin Ya Kashe Mahaifiyar Shi

Innalillahi wa inna ilaihirraji’un tofah masu saurare yauma dai kamar kullum taskar nasaba tazo maku da wani abun ban mamaki kuma abun takaici da Allah wadai.
A yau ne mukasamu rahoton cewa wani matashi dan shekara ashirin da aikata wata mummunar ta’ada lamarin dai yafaru ne a unguwar fadama dake rijiyar lemo karamar hukumar Ungoggo.
Matashin dai ya shiga gidan mahaifinsa ne inda yatarar da matar baban shi da ita da yarta mai shekera takwas yakama uwar yarinyar ya sassarata sannan daga bisani ganin cewa yarinyar taga sanda ya aikata wannan ya’asa itama yakamata ya sassarata.
Mijin matar maisuna sagir mai magani shi ne yayi arba da gawarwakin lokacin da yashigo gidan,matashin dai ya bayyana dalilansa da sukasa ya aikata wannan aika-aika acewar shi aiwannan matar itace tayi sanadiyyar fitar da mahaifiyar shi a wannan gida.
KARIN BAYANI:
To masu saurare kun daiji wannan al’amari da yafaru anan sai muce Allah yashiga tsakanin nagari da mugu kuma masu irin wannan hali Allah yashirye su ameen.
Kar kumanta zaku iya bayyana mana ra’ayoyinku a wannan taaha tamu mai al barka mungode.