Labarai

Yanzu-Yanzu:- Ranar litinin zaa yan kewa Abduljabbar Hukuncin kisa ta hanyar rataya

@Shari’ar Mal. Abduljabbar Kabara…

Danna Wannan link domin kallon Bidiyon👇https://fb.watch/hUcIqoncW2/

A gobe alhamis 15th, December 2022 ake saka ran kammala shari’ar Mal. Sarki.

Na kasa yadda musulmin kirki koda ac

e jahili ne a cikin musulmai zai iya buɗa baki ya zagi Annabi ﷺ, balle wanda ya amsa sunan musulmi kuma mai ilimi, wanda ya taso a gidan ilmi, ya samu tarbiyya daga uba irin Mal. Nasir Kabara Rahimahullah.

Duk saɓanin mu da mutum muna fatan Allah ya tsare mu ƙiyayyar sa bisa son zuciyar mu, da kuma qin yi masa adalci koda a magana ne, Allah Swt yace ;

وَإِذَا قُلْتُمْ فَاعْدِلُوا

“yayin da zakuyi furuci (akan wani to) to kuyi magana ta adalci…”

Suratu An’am 6/152.

Malam Abduljabbar Kabara mutum ne kamar kowa wanda zai iya dai dai kuma zai iya kuskure, amma tsantsar zalunci ne jifan musulmi da cewa ya zagi Annabi ﷺ, kuma abinda yake bayyanar da tsantsar rashin adalci a cikin lamarin shine da aka qi bayyana gaskiya Mal. Abduljabbar ko ɗaya, bayan an san dole akwai gaskiya a cikin wasu abubuwan da yake korewa da aka raɓa shi da Shugaba Alayhis Salaam.

Sunnar adamiyya ce kuskure, kamar yadda rashin yin kuskure ma’asumanci ne kuma hakan kaɗai ya keɓanta ne da Annabawan Allah da mala’ikun sa, bayan su kuma babu mai wannan matsayin a cikin halitta kaf.

Bawai goyon bayan Mal. Abduljabbar nake ba gaskiya nake goyan baya, da kuma kishin irin abubuwan da ake raɓawa Annabi marasa kyau da sunan ilimi ko addini.

Idan har gaskiya ne an tabbatar da laifin M. Abduljabbar Kabara to me ya hana tuntuni a yanke masa hukunci?

Babu wata shari’a da za’ai tsawon shekara ana yi ace an rasa gane mai gaskiya, sai dai idan akwai wata manufa a cikin ta bawai gaskiyar ake nema ba.

Fatana a cikin wannan shari’ar shine Allah ya bayyana gaskiya a duk inda take, duk kuma masu hannu cikin zaluntar bawan Allah nan da masu makirci Allah yabi masa haqqin sa, dama wata shari’ar sai a lahira.

Amma bazan taɓa yadda M. Abduljabbar ya zagi Annabi ﷺ ba ko a mafarki, banji da kunne na ba, dan haka dan wani ya faɗa bazan yadda dashi ba.

Muna son Annabi Muhammad ﷺ fiye da son komai, kuma muna kishin sa fiye da komai, muna tare da mai girmama mana shi da kishin sa a ko ina yake, fansar kulliyya mukai gare shi.

Khalifa Habeebu Rasulullah
Wednesday, December 2022.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button