Labarai

Subahanallah😭 Yanzu-Yanzu Rikicin Limanci Ya 6arke A Masallacin Marigayi Dr. Ahmad B.u.k

Al’amura sun soma komawa daidai a unguwar Tudun Yola da ke Kano.

 

Rikicin jagoranci ya tilasta rashin yin sallar Jumu’a a Masallacin Darul Hadith na marigayi Dr. Ahmad Ibrahim BUK.

Tarzoma ta kaure a Masallacin ne lokacin da sabon liman zai hau Mumbari don soma huɗu ba, inda wasu fusatattu suka janyo rigarsa ta baya don nuna ƙin amincewa da shi, lamarin da ya kawo rikici.

Tuni aka rufe masallacin tare da baza jami’an tsaro a kofa da kewayensa.

 

Yanzu haka dai tuni ɓangarorin biyu suka nufi shalkwatar ƴan sanda da ke Bompai domin sasantawa.

Muna tare da ƙarin bayani nan gaba.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button