WASANNI
Trending

Ronaldo ya yi suɓul-da-baka a gaban magoya bayan ƙungiyar inda ya ce ‘South Afirka’ a maimakon ‘Saudi Arabiya’.

Ronaldo ya yi suɓutar-baki a Saudiyya

 

Shahararren ɗan ƙwallon ƙafar duniya Cristiano Ronaldo ya yi tuntuɓen harshe a lokacin da ake gabatar da shi ga sabuwar ƙungiyar da ya koma ta Al Nassr ranar Talata,

 

Ronaldo ya yi suɓul-da-baka a gaban magoya bayan ƙungiyar inda ya ce ‘South Afirka’ a maimakon ‘Saudi Arabiya’.

 

Ɗan wasan ya koma Al Nassr ranar Juma’a bayan da ya raba-gari da tsohuwar ƙungiyarsa Manchester United.

 

Ronaldo ya ce: “Wasan ƙwallon ƙafa wani abu ne na daban, dan haka zuwana ‘South Afrika’ ba shi ne ke nuna cewa ta-ƙare min ba”

 

”Wannan shi ne dalilin da ya sa nake son samun sauyi, haƙiƙa ban damu da abin da mutane ke cewa ba”, kamar yadda Ronaldo ya bayyana wa manema labarai a lokacin da aka gabatar da shi a birnin Riyadh.

 

Ya ƙara da cewa: “Na samu komai, na yi wasa a manyan ƙungiyoyi a Turai, a yanzu kuma lokacin buɗe sabon babi ne a Asiya”.

 

Bayan taron manema labaran, ɗan wasan ya sanya sabuwar rigar wasansa ta ƙungiyar a filin wasan a gaban dubban magoya bayanta.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button