An yankewa Wani Matashi Hannun Shi Awajan Rabon Fada

Wani matashi dan shekara 23 mai suna Salisu hussaini anyanke masa hannun shi ne awajan rabon wani fada yakuma bayyana hakan amatsayin babbar jarabawa
Wannan matashi nidai sana’ar dainki nakeyi aranar antashi inata farinciki babu abunda yake damuna kuma babu abunda yake muni ciwo arayiwa natashi natafi wajan sana’a ta domin cigaba da aiki.
Awannnan ranar saida mukakai har dare muna aiki misalin karfe tara nadare9:00 pm sai narufe shago dani da maigidana domin mukai wani kayan da mukagamada su.
Ina zaune saiji hayaniya awake sai nafita natarar da mutum biyu suna fada nan take nashiga tsakiyarsu domin raba fadan.
Kawai sai yadauko wuka yacakamun ahannu ganin yadda jini kezuba sosai sai sukagudu
Akakaini asibitin dala likita yace sai anyanke hannu domin kuwa jijiyar jini ce ta tsinke
Acewarsa ahaka Allah yajarabceni narasa hannu na awjan aikin alkhairi raba fada domin sulhunta tsakanin mutum biyu.
Yakuma nemi taimakon yan uwa mza da mata sutaya shi addu’a Allah yarabamu da mummunar kaddara, ameen.