SIYASA

An Kori Hamza Al-Mustafa Da Wasu Yan Takara a Jam’iyyar AA Party ||Kotu

A wani rahoto da muka samu; wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta janye hukuncin da ta yanke a ranar 4 ga watan Nuwamba na amincewa da ‘yan takarar da jagorancin Dr Adekunle Rufa’i Omo-Aje ya jagoranta na jam’iyyar Action Alliance (AA) a yau Alhamis.

Mai shari’a Zainab Abubakar a hukuncin da ta yanke ta ce karar da Kenneth Obidiche Udeze ke jagoranta ya shigar ba ta inganta ba.

Mai shari’ar tun a ranar 4 ga watan Nuwamba ta umarci hukumar zabe mai zaman kanta INEC da ta amince da yan takarar na jam’iyyar AA ya gabatar domin zaɓen 2023 mai zuwa.

Mai shari’ar ta kuma umurci INEC da ta yi watsi da ƴan takarar da shugabancin Udeze ya gabatar daga cikinsu har da Manjo Hamzat Al-Mustapha mai neman takarar shugaban kasa.

Amma Udeze, wanda aka amince da dakatarwarsa da kuma korar shi a matsayin shugaban AA na kasa a wasu hukunce-hukunce guda biyu na kotun daukaka kara, ya bukaci babbar kotun ta Abuja da ta janye hukuncin na ranar 4 ga watan Nuwamba inda yake cewa; an same shi ta hanyar zamba ne, kuma yana mai ikirarin cewa har yanzu shi ne shugaban jam’iyyar na kasa.

Da ta ke yanke hukuncin a yau, Mai shari’a Zainab ta ce; bayan hukuncin kotun daukaka kara biyu da kuma wani hukuncin da babbar kotun tarayya ta yanke a Abeokuta, Udeze ba zai iya yin ikirarin cewa shi ne shugaban jam’iyyar ba a bisa doka.

Hukunce hukunce guda biyu na Kotun Daukaka Kara an yanke su ne a ranar 7 ga watan Janairu da 11 ga watan Nuwamba, yayin da kotun Abeokuta ta yanke hukuncin a ranar 8 ga watan Satumba, ƙarƙashin mai shari’a J. O. Abdulmalik a cikin wata kara mai lamba: FHC/AB/CS/120/2022.

 

Alkalin kotun ta kara da cewa; hukuncin da ta yanke a ranar 4 ga watan Nuwamba bai samu ta hanyar zamba ba kamar yadda Udeze ya yi zargi.

Ta kara da bayyana Udeze a matsayin mutum ne mai cike da ruɗani kuma mai shiga tsakani, ya na kokarin tsoma baki a harkokin jam’iyyar da aka dakatar da shi daga bisani kuma aka kore shi, dan haka Zainab ta yi watsi da karar.

Idan za ku tuna, Manjo Al-Mustapha, ne ya lashe zaben fidda gwanin takarar shugaban kasa na jam’iyyar da bangaren Udeze suka gudanar da jimillar kuri’u 506, inda ya doke Samson Odupitan wanda shi ne abokin hamayyarsa tilo a ranar 9 ga watan Yuni a Abuja.

Ku kasance damu dan samun labarai masu inganci.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button