Hausa Films
Trending

LABARINA SEASON 5 EPISODE 14

Shahararren shirin nan mai farin jini wato LABARINA yadau zafi, duba da yanda aka tsaya daidai wurinda Baba Dan yasha shaka yana kakarin mutuwa, hakan ne yasa makallata wannan shiri ke ta zumudin kallon cigaban wannan shiri, saidai kuma Director wannan shiri Malam Aminu Saira Ya fitar da wata sanar wa a shafin sa na Instagram, kamar yadda yace cewa;

SANARWA KANA SHIRIN LABARINA SEASON 6. Assalamu alaikum  masoya wannan shiri, kamar yadda muka sanar a karshen episode din da ya gaba ta cewa mun kammala Season 5. Insha Allah 16 ga wannan watan da muke ciki na Disamba zamu cigaba da kawo muku Season 6 a wuraren da muka saba haskawa. Muna godiya sosai a gareku masoya, Allah yabar zumunci Saira Movies.

ƘARIN BAYANI

Sanarwar da Director Aminu Saira ya fitar ya nuna cewa; sun tafi hutu amma ba mai dadewa bane kamar yadda aka saba, zasu dawo ranar 16 ga watan da muke ciki na ƙarshe shekara 2022 wato watan December, kamar yadda ya bayyana.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button