Labarai

Katsina; Yanzu Yanzu Ƴan Bindiga Sun Sace Jama’a A Masallaci

A wani rahoto da muka samu mun samu labarin cewa; yan bindiga sun kai hari a masallaci, inda suka sace jama’a sama da ashirin 20 a ƙauyen Maigamji dake ƙaramar hukumar Funtua a jihar Katsina Nigeria.

Maharan sun kai harine a ranar Asabar da daddare yayin da ake sallar Isha’i.

Jami’in tsaro sun tabbatar da faruwar lamarin, kamar yadda mai magana da yawun yan sandan jihar Katsina SP Gambo Isah ya shaidawa manema labarai cewa; yan bindiga sun raunata mutum biyar harda limamin masallacin, amma an sallamosu daga asibiti, ya kara da cewa an jami’an tsaro da yan sakai sun samu nasarar kwato wasu daga cikin wadanda aka sace.

Ya cigaba da cewa; saidai akwai mutum 13  da ba’a gani ba har yanzu, amma ana iya bakin kokari domin aka an kubutar da ragowar mutanen dake hannun yan ta’addan, kamar yanda SP yace.

KARIN BAYANI

Al’amarin ta’addanci da garkuwa da mutane dan neman kudin fansa ya zama ƙarfen ƙafa a wasu yankuna dake arewa cin Nigeria, ciki harda Jihar Katsina wadda itace mahaifar Shugaban Kasa Muhammadu Buhari. Gashi kuma zabe na kara ƙaratowa a kasar, muna fata wannan zaɓe ya zama silar garuwar Nigeria.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button