LabaraiSIYASAUncategorized

Anyiwa Mubarak Uniquepikin Bulala 20 Tare Da Hukunci Mai Tsauri

An yankewa Mubarak Uniquepikin hukuncin Bulala ashirin dashi da Nazifi Muhammad Bala a kotun majesty a kano.

 

Bayan katobara da yan tiktok din suka jawowa kansu na cin Mutumcin mai girma Dr Abdullahi Umar Ganduje a manhajar tiktok yaudai an yake musu hukunci Har Guda 4 Wanda hukuncin ya hadar da:-

1) Kotu ta nemi dasu bayar da tarar Dubu 10000 ko wannen su

2) an kara cinsu tarar 10000 saboda neman tada zaune tsaye da sukai zasu bada Dubu 20,000 Kenan kowannen su.

3) kotu ta umarcesu da zasu ringa share kotun na tsawon kwana 30 harda ranakun asabar da Lahadi kuma harda wankin Toilets da komai da komai, sannan kuma kotu tayi musu Bulala ashirin ashirin.

4) kotu ta umarcesu da suje social media suyi video na bada hakurin cin Mutumcin da sukayiwa Gwannan Duniya ta gani.

Wannan shine shukuncin da kotu ta yanke masu domin hakan ya zama izna ga masu shirin yin batanci ga gwamnati, saidai muce Allah ya kyauta ya kuma kiyaye gaba.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button