KannywoodLabarai

An Tura Mubarak Uniquepikin Gidan Yari Sanadiyyar Cin Mutumcin Ganduje

 

An garqame matashin mai wasan barkwamci a shafin tiktok wato mubarak_uniquepikin bayan sake wani Bidiyo da yayi wanda yaci mutumcin Gwannan Kano dr Abdullahi Umar Ganduje.

 

Matashin yayi bidiyon ne da niyyar barkwamci kamar yadda ya saba, saidai wannan yasa bam-bam domin kuwa wasu suna ganin akwai cin fuska a bidiyon ganin yadda ya kira sunnan Gwannan kiri-kiri harma da matarsa, sanadiyyar hakanne hukumar tace fina-finai ta antayashi kotu.

 

Saidai tun kafin faruwar hakan mubarak_uniquepikin ya sauke bidiyon ta’asar da yayi a shafin nasa, amma hakan bai hana bidiyon yaduwaba kasantuwar dole wasu zasu dauki bidiyon Kuda kuwa minti 1 yayi akai, musamman yadda bidiyon ya kasance irin wannan.

Bayan faruwar hakanne yan uwansa masu wasan barkwamci suketa bawa Gwannan hakuri akan cewa kuskure ne kuma hakan zabai sake faruwaba ayi hakuri a sako musu Dan uwansu,

Ka bidiyon yadda abin ya faru👇

https://youtu.be/aobjN957vm8

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button