Labarai

MALAMAI SUNYI CA KAN BATUN CANJA TAKARDAR NAIRA A NIGERIA

An samu tabbacin kin canza ajamin jikin naira kamar yadda wasu suke tunanin hakan, daga bakin Muhammadu Sunusi II.

 

A rade radin da yake gudana a kafafen sada zumunta na Canza naira a Nigeria, wasu daga cikin malamai da jama’a suna ganin anyi hakan ne domin a cire rubutun ajami dake jikin naira, saidai an gano tabbacin Baza a cire rubutun ajamin ba daga bakin Muhammadu Sunusi II Inda ya tabbatar wa da duniya hakan bayan zantawarsa da Gwannan Banki na yanzu Godwin Emefiele.

Saidai hakan bai dakatar da maganganun ba, Inda malaman suna ganin cewa shi kansa canza takardar Naira din bai dace ba, sun kawo dalilinsu na cewa anyi hakan a baya kuma hakan bai haifar da mai ido ba saboda haka matukar hakan ba dole bane to a dakatar da hakan. sannan sunyi nuni da cewa a baya anyi hakan lokacin mulkin Shugaba Muhammadu Buhari na farko mulkin soja, hakan ya janyo asara mai yawa.

Amma a karo na biyu sun kara da cewa amma idan yanayi da tsarin da Goodluck yabi za’ayi to hakan yayi saboda yayi nasa kuma hakan bai haifar da matsalaba.

Idan bamu mantaba a mulkin Goodluck an canza naira Dari kuma canjin bai haifar da matsalaba don anbi hanyar daya dace hanyar kuma itace kamar haka, An can naira ₦100 ta hanyar duk kudin da suka shiga Banki bazasu fitoba kuma ba’a daina amsar tsohuwarba har ta bace Wanda yanzu haka mutane sukan ganta jifa-jifa kuma harwayau ba’a daina amsartaba, matukar wannan tsari za’abi to sun goyi bayan hakan.

Ga Bidiyon da Muhammadu Sunusi II ya bayyana hakan

https://youtu.be/KYn5_1o-4yE

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button