Labarai

Wani Ango Ya Rasu Bayan An Daura Auren Sa Da Sa’o’i kaɗan

Innalillahi wani ango ya riga mu gidan gaskiya sa’o’i kaɗan bayan daura auren sa, kamar yadda muka samu rahoto angon matashi mai suna Shehu Lili Kofar Atiku ya rasu bayan daura auren sa da sa’o’i ashirin da hudu (washe gari bayan daura masa aure.)

kamar yadda abokin angon mai suna Shamsuddeen Buratai shine ya tabbatar da faruwar haka a garin Sokoto.

Abokin ango Shamsuddeen ya bayyana cewa abokin nasa ango Shehu Lili Kofar Atiku ya rasu bayan fama da yar garejiyar rashin lafiya.

Abokin angon ya kara da cewa an daura auren ranar Lahadi kuma angon ya rasu washe ranar Litinin bayan sa’o’i ashirin da hudu.

Shamsuddeen Buratai ya cigaba da cewa;

“Shehu abokina ne tun na yarinta kuma dan’uwa na tsawon fiye da shekara 30. Yana fama da matsananciyar malaria wacce take taso masa duk lokacin sanyi. Kamar kowace shekara, ciwon nasa ya taso masa a bana a cikin watan Disamba, inda ya sha magunguna ya samu lafiya.”

“Da safiyar yau misalin karfe tara na safe, ya fito inda muka gaisa yadda muka saba. Kwatsam kawai sai ya fara jin wani bakon yanayi inda yace manan yana tunanin ciwon malaria ne yake kokarin dawo masa. Kafin mu yi aune kawai har ya fadi kasa, shikenan karshen sa kenan.”

#LabarunHausa

Anyi jana’izar marigayin ango kamar yadda addinin musulunci ya tanada.

Muna fata Allah ya jikansa ya gafarta masa.

TUNATARWA

Dan uwa karka shagala wajen neman duniya har ka manta da lahirar ka, saboda baka san yaushe be ajlin ka ba, bar ganin Kanada koshin lafiya, da dama sun mutu ba tareda wata rashin lafiya ba, Allah yasa mu dace.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button