Labarai

ABINDA YASA RARARA YAYIWA GANDUJE BORE

Rikicin cikin gida ya barke tsakanin Mawaki Rarara da kuma maigirma Gwamnan Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje,

Idan mukayi la’akari da yanda mawakin yaketa barin wakoki kuma baya saka Gandujen aciki saidai Kawai ya wake Bola Ahmad Tuninbu wannan zai tabbatar mana cewa sun samu matsala, bugu da Kari acikin wasu wakokin nasa yana sukar gwamnatin.

Wadannan dalilai sune suka saka wasu daga Cikin mabiya Ganduje suke kokari wajen ganin sun hana Mawaki Rarara Rawar gaban hantsi, Inda suka sha alwashin cewa sunsan tafiyar APC a kano dole saida mai girma Dr Abdullahi Umar Ganduje saboda haka Tuninbu bazai dauki Rogo ya kyale kitse ba ma’ana Baza’a Dauki Rarara ba abar Dr Abdullahi Umar Ganduje.

Duba da yanayin tabargazar da rara yake yungurin aikatawa na Fada da gwannati duda kasancewar ba bakon abu bane a wajensa Wai idan da Sabo ya saba, Saidai a wannan karon magoya Bayan Dr Abdullahi Umar Ganduje sunce wai fada da aljani ba dadi kuma idan akayi baza aci riba ba matukar yace zaiyi musu butulci to babu shakka sai kashinsa ya bushe domin su bazai musu halin kolo ba su kyaleshi, Wanda sanadiyyar haka ne wani mawaki yaci alwashin tone asirin rarara rankatakaf Inda ya sake wata wakarsa mai taken tuna asiri, kuma tonon asirinne kwarai acikin wakar abinda ya danganci lokacin da yake kolo da yanda ya gudarin da karatun nasa na makarantar allo, saidai mawakin ya amsa cewa shi kolone amma ya mayar da martanin wasu abubuwa da bai aminta dasu ba da aka fada akansa.

 

SUWA RARARA YAYIWA BUTULCI.
1. Malam Ibrahim Shekarau
2. Rabi’u Musa Kwankwaso
3. Dr Abdullahi Umar Ganduje

 

DALILIN DA YASA YAYI MUSU BUTULCI

1. MALAM IBRAHIM SHEKARAU
Shekarau Yayi gwamna a kano a shekarar 2003 – 2011 Wanda a lokacin Rarara yayi masa wakoki bula adadin saidai bayan saukarsa daga mulki sai akaji mawakin Yana sukarsa wanda wasu basusan daliliba kawai sai suka Kira abin da Butulci wanda a zahirin gaskiya abin ba haka yakeba,

Tun talili a lokacin baya T Gwarzo shine mai gida a wurin Rarara hasalima ta dalilinsa ya shigo harkar siyasa, kuma a lokacin da Malam Ibrahim Shekarau yana kan mulki kwarai da gaske duniya ta gani ya taka muhimmiyar rawa ta gani ta fada wajan tafiyar da mulkin wanda lokacin Da Malam Ibrahim Shekarau ya kare mulki shi yakamata a tsayar dan takara amma Hakan ta faskara Shekarau ya dakko SALUHU SAGIR TAKAI ya bashi takara wanda a lokacin Rarara ya wakoki wadanda suke nunin cewa wakan bai daceba saidai Malam Ibrahim Shekarau bai jisaba ganin hakanne daya tabbatar baza a Bawa gwanin nasa takararba ya rero wata waka mai taken ta bare bada muba wanda mutane sukaita kace nace akan wakar suke cewa yayi Butulci.

2. Rabi’u Musa Kwankwaso
Dan Musa Kenan yayi Gwamnan Kano karo na biyu a shekarar 2011 – 2015 wanda a wannan lokaci ne rarara ya dawo yimasa waka bayan yayiwa Shekarau Butulci kamar yanda Jama’a suke fadi, inda Shima daga bisani ya gujeshi bayan da suka Samu matsala tsakanin kwankwaso da ganduje.
Saidai a wannan karon abin yasa babban dana baya domin kuma babu wani abu wanda kwankwaso yayiwa Rarara, kawai dai a lokacin mawakin yabi Gwamnati ne to babu laifi idan an Kira wannan da Butulci kuma rarara kwarai bai kyautaba a wannan karo.

 

3. DR ABDULLAHI UMAR GANDUJE
Ya fara mulki ne bayan da kwankwaso ya gama a shekara ta 2015 – 2023, Shima gwannan yana daya daga cikin gwamnonin da mawaki rarara ya rera musu waka domin mawakin ya rera wa Ganduje wakoki bila adadin, saidai a karshen shekara ta 2022 ne akaji mawakin yanatayin wakoki Amma baya saka Gwamnan a ciki kuma kasantuwarsu a Cikin Jam’iyya daya bai kamata hakan ta faruba matukar ana zaune kalau, hakan ne zai nuna Maka cewa kwarai sun sami matsala.

Bugu da Kari ganin yanda mawakin yake kokarin watsawa gwamnatin kasa a ido hakan yasa wasu daga cikin na jikin Gwamnan suke kokari wajen ganin sun hana mawakin rawar gaban hantsi idan har wata majiya ta fito Wanda ake kokarin rushe gidan mawakin a garin Kano, saidai kuma ana cikin hakan ne sai aka tsinci wani karamin bidiyon mawakin wanda ya karade social media Bidiyon kuwa bidiyo ne na wakar mawakin yanata tikar rawa abinsa tare da magana cikin habaici sannan Yan Amshin wakar sanye suke da Kaya irin na fulani wanda duka alamomi sun nuna cewa da Gwamnan yake kasantuwarsa Dan Fulani kwarai wannan bidiyo ya janyo cece kuce.

Saidai An Gano cewa mawakin ya nemi wata bukata ne a wajen Gwamnatin inda aka kasa biya masa wannan bukata kuwa itace ya nemi da a tsayar da wasu Yan takara amma akaki amincewa da bukatarsa shi kuma ganin yanda ya bada gutum muwa a tafiyar Bai kamata ace ya nemi alfarma a Karo na farko ba Amma anki cika masa, wannan ya nuna cewa bashi da muhinmanci a tafiyar kenan tunda Har zai kawo kudirinsa Karo na farko Amma abin yaci tira kuma babu wani kwakwkwaran dalilin hakan, Hakan ne yasa yaja baya baya.

Allah ya kyauta, wannan shine kadan daga Cikin abinda yake faruwa.

Kasance da Taskar Nasaba Domin samin Ingantattu kuma sahihan labarai

 

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button