Labarai

YADDA AKA GUDANAR DA DAURIN AUREN SHEKH AMINU DAURAWA

YADDA AKA GUDANAR DA DAURIN AUREN SHEKH AMINU DAURAWA

 

An daura Auren Shekh Aminu Daurawa ne tare da amaryarsa Haulat Aminu Ishaq a ranar Juma’a 21 ga watan October na shekarar 2022 a babban Masallachin juma’a dake Garin Gusau Jihar Zamfara.

 

 

Kafin Daurin Auren Malam Aminu Daurarawa ya gabatar da fadakarwa mai taken Sallah da Muhimmancinta, Shiri ne da Ma’aikatar Shari’a da harkokin Addini ke gabatarwa duk ranar Juma’a a Masallachin na Gusau, Zamfara State, Bayan kammala wannan fadakarwa ne aka gudanar da daurin auren, Inda daga bisani Bayan daurin auren keda wuya aka rankaya gidan Gwamnati domin gudanar da Walimar bikin.

 

 

 

 

 

Daurin Auren ya Samu Halartar manya-manyan Malamai dama sauran masu fada aji kuma an gudanar da daurin auren Cikin koshin lapiya da kwanciyar hankali.

 

 

 

An kawo Amarya Gidan Mijinta saidai fatan Allah ya bada Zaman lafiya da kwanciyar hankali ya kuma kawo zuri’a dayyiba.

 

 

 

Bayan wanyewar biki ne Malam Aminu Daurarawa ya fito Cikin raha yana mai bawa wadanda ya kasa hakuri tare da godiya ga dumbin Jama’ar da suka Bada kudummuwarsu da fannoni da dama kwarai da gaske yana Godiya Cikin kakkausar murya

 

Madallah, Allah Ya Bada Zaman Lapiya

 

Ga Bidiyon DAURIN AUREN👇

https://youtu.be/OepaXlUTCXk

 

 

 

 

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button