Tech

AN KADDAMAR DA 5G NETWORK A NIGERIA

AN KADDAMAR DA 5G NETWORK A NIGERIA.

 

A jiya ne 20 ga watan October na shekarar  2022 Shekh Isah Ali Ibrahim Pantami ya yayi jawabi cikakke kuma mai fa’ida gameda samuwar 5G NETWORK a Nigeria.

 

Minister of Communications and Digital Economy’ professor Isah Ali Ibrahim Pantami yayi murna kwarai matuka sannan yayi bayani dalla-dallah Dan gane da amfani da kuma muhimmancin 5G network a wajen jama’a musamma duba da yadda abubuwa rankatakaf suke yunkurin komawa online.

 

 

Sannan bugu da Kari Nigeria tana daya daga Cikin jerin kasashen da suke da 5G network a Duniya a dai_dai wannan lokaci, kwarai babu shakka wannan abun alfaharine ka daukacin Jama’ar kasar.

I

 

Kasar Nigeria suna Matukar alfahari da Kafanin layi na MTN domin a sanadiyyar sune kasar ta Samu wannan babban cigaba na samun 5G Network, kuma a taron da aka gudanar wanda Shekh Isah Ali Ibrahim Pantami ya Samu halarta an bayyana cewa gab 5G network din yake da fara aiki a kasar ta Nigeria.

 

Menene 5G NETWORK

5G network shine ƙarni na biyar na cibiyoyin sadarwar salula. Har zuwa sau 100 cikin sauri fiye da 4G network, 5G network ba’a taɓa ƙirƙirar wani cibiyar sadarwa Sama dashi ba a Duniya Hasalima dai shine karshe.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button