
Matsahi ya zama millionaire a rana daya, inda yayi nasarar cinye cacar daya shiga da Naira ₦800 kacal, kuma ya lashe Naira miliyan talatin da takwas (38,000,000) bayan yasa Naira dari takwas kacal.
Matashin ya nuna farin cikin sa a fili sosai bayan ya zama muluniya a rana daya, inda ya garzaya yayi alwala ya tafi Masallaci domin godiya ga Allah.
Jama’a masu taya shi murna maza da mata sun cira unguwar tasu, inda ake zuwa ana tayashi murna tareda gani da ido, domin Hausawa sunce “Gani ya kori ji” kamar yadda zaku gani a wannan video, a cikin video da aka wallafa a shafin Twitter zakuga yanda jama’a maza da mata sukayi cincirindo a kofar shagon nasa.
Yan mata sun mato akan sabon millionaire inda suka bishi har gun da yake alwala tareda binsa gun da yake Sallah.
https://twitter.com/AduraGbhemie/status/1582308399790030848?t=8F85e8uBocB7085-E4bgpw&s=19
KARIN BAYANI
Matashin yayi nasarar lashe wadannan kudadene a cacar da ya shiga a shafin Bet9ja.
Ku kasance da wannan shafi don samun labarai masu inganci.
Mungode!